Babbar jami'ar hukumar yawon bude ido ta Afrika ta kudu Amanda Kotze-Nhlapo, ta bayyana hakan a jiya Litinin yayin wani taron Afrika na shekarar 2019 wanda ya shafi batun bunakasa fannin yawon bude ido na Afrika wanda aka gudanar a lekgotla na birnin Johannesburg.
Ta ce, "Akwai masu sha'awar fannin yawon bude ido daga Afrika kana akwai su daga sauran sassan duniya. Don haka muka gayyaci dukkan masu sha'awar bunkasa wannan kasuwa da nufin ciyar da shiyyarmu da kuma nahiyarmu gaba."
Fiona Opati-Namiti, darakatar hukumar Villa Rosa ta kasar Kenya, ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ya kamata kasashen Afrika su hada gwiwa don yin magana da murya daya ga duniya kuma su yi hadin gwiwa wajen karbar bakuncin muhimman tarurruka kuma dole ne su kawar da dukkan wasu kalubaloli dake kawo cikas ga fannin yawon bude ido kamar batun ka'idojin neman takardun izini na biza. (Ahmad)