A wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron, shugabannin kasashen Larabawan da na Turai sun bayyana kudurinsu na karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a matakin koli da kuma sauran bangarorin hadin gwiwa a tsakaninsu.
Shugabannin sun sake jaddada aniyarsu na kyautata hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa bisa ga tsarin kasa da kasa da kuma mutunta dokokin kasa da kasa domin dakile kalubalolin dake addabar duniya, wanda ya kunshi hadin gwiwa tsakanin LAS, EU, MDD da AU. (Ahmad)