in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Yankin manyan tafkunan Afrika na kan hanyar farfadowa
2019-02-26 09:27:49 cri

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yankin manyan tafkunan Afrika da ya fuskanci rikice-rikice tsawon gomman shekaru, yana kan hanyarsa na farfadowa, tana mai alakanta hakan da rawar da kungiyoiyin yankin da na kasashen waje suka taka wajen tabbatar da mika mulki lami lafiya.

Manzon musammam na Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a yankin manyan tafkunan Afrika Said Djinnit ne ya bayyana haka jiya Litinin 25 ga wata, inda ya ce, aiwatar da tsarin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a zuciyar nahiyar, ya fara aiki.

Said Djinnit ya kara da cewa yankin na samun ci gaba, kuma ana hada hannu wajen magance abubuwan dake barazana ga zaman lafiya. Yana mai cewa, idan aka yi nasarar wanzar da zaman lafiya a yankin, to dukkan nahiyar za ta amfana.

Jami'in ci gaba da cewa, sauya tsarin hukumomin gwamnati da gudanar da sahihan zabe da tafiya tare da kowa, su ne abubuwan da suka gaggauta sake gina kasashen yankin da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Burundi da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China