in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren harkokin wajen Amurka: Za a sanyawa Venezuela karin takunkumi
2019-02-25 15:02:39 cri

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada a jiya Lahadi cewa Amurka za ta sanya karin takunkumi kan kasar Venezuela.

Za'a gudanar da taron Lima Group a ranar Litinin, inda za'a kammala daukar sauran matakai. Akwai wasu karin takunkumai da za'a sanya, in ji Pompeo ya furta hakan ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na CNN.

Mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence zai tafi zuwa jihar Colombia a ranar 25 ga watan Fabrairu domin halartar taron na Lima Group a madadin shugaban kasar Amurka Donald Trump, fadar White House ne ta sanar da hakan a ranar Alhamis.

Taron na Lima Group, ya kunshi kasashe 13 na yankin Latin Amurka da Canada, kungiya ce ta gamayyar kasa da kasa ta aka kafa a watan Agustan shekarar 2017, za su tattauna game da halin da ake ciki a kasar Venezuela.

Pompeo ya bayyana cewa Amurka za ta samar da karin kayayyakin tallafin jin kai ga mutanen Venezuela, yana mai cewa, madugun adawar kasar Juan Guaido shi ne ya mika bukatar neman tallafin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China