in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci shugabannin kasashen Larabawa da na Turai su hada hannu wajen tunkarar kalubalen da suke fuskanta
2019-02-25 13:31:52 cri
Shugabannin kasashen Turai da na Larabawa, sun jaddada bukatar kara hada hannu wajen tunkarar kalubale iri guda da suke fuskanta.

Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar kawancen kasashen Larabawa da Tarayyar Turai, ke gudanar da taro karon farko, wanda aka kaddamar jiya Lahadi a birnin Shar el Sheiklh na kasar Masar.

A jawabinsa na bude taron na yini biyu da za a kammala yau Litinin, shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ce ta'addanci na bazuwa tamkar wutar daji, yana mai bukatar shugabannin su hada hannu wajen yakarsa.

Ya ce ya kamata su kara tabbatar da hadin kansu domin tunkarar barazanar tare da bata da hujja.

Da yake tsokaci game da batun kwararar bakin haure daga kasashen Larabawa zuwa Turai, Shugaba ai-Sisi ya ce ya kamata a magance matsalar ta hanyar hadin gwiwa.

Shi kuwa shugaban majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk cewa ya yi, akwai bukatar shugabannin kasashen Larabawa da na Turai su tunkari kalubale iri guda da suke fuskanta, su kuma yi amfani da damarmakin da yanayin kasa da tarihi suka samar.

Ya ce a lokacin da ake samun karuwar fargaba, shugabannin Turai da na Larabawa na bukatar aiki tare domin samar da kwanciyar hankali mai dorewa, tare da ba al'ummominsu tabbacin samun zaman lafiya da ci gaba da suka cancanci samu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China