in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Senegal: An sake zabar Macky Sall a matsayin shugaban kasar
2019-02-25 11:06:07 cri

Firaministan kasar Senegal Mahammed Boun Abdallah Dionne, ya sanar da safiyar yau Litinin cewa, an sake zabar Macky Sall a matsayin shugaban kasar bayan samun sakamakon farko farko na zaben shugaban kasar.

A cewar firaministan kasar ta Senegal, Macky Sall ya samu kashi 57 bisa 100 na kuri'un da aka kada a duk fadin kasar kuma shi ne ya lashe zaben.

A wata sanarwa da aka baiwa manema labarai a hedkwatar cibiyar 'yan jaridu na dan takarar Macky Sall, Dionne ya ce, bisa ga sakamakon da aka tattara daga yankunan kasar, Macky Sall shi ne dan takarar dake kan gaba.

Dionne ya ce, shugaban kasar mai ci shi ne yake kan gaba a yankunan mazabu 13 daga cikin mazabu 14 na kasar.

To sai dai kuma, sakamakon zaben da firaministan kasar ya yada a kafafen yada labaran shi ne na farko da aka yada a kasar ba tare da samun amincewar hukumomin zaben kasar ba.

Kafin wannan kuma, 'yan takarar jam'iyyun adawar kasar Idrissa Seck da Ousmane Sonko suka kira taron manema labarai, inda suka yi watsi da sanarwar da aka yada a kafafen yada labaran, wanda ta baiwa Macky Sall nasara a zaben.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China