in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta kudu ya kafa kotun musamman ta yaki da rashawa
2019-02-25 10:29:56 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana a ranar Lahadi, cewar ya kafa wata kotun musamman ta yaki da ayyukan rashawa a kasar.

Fadar shugaban kasar ta ce, an kafa kotun ne da nufin kammala dukkan shari'un da suka jibinci cin amanar kasa wadanda ake fatan kammala su cikin gaggawa bayan kwamitocin bincike na musamman wato (SIU) sun kammala ayyukansu.

A cewar sanarwar, wadannan laifuka da kwamitin SIU ya kammala aiki kansu sun kunshi dukkan yarjejeniyoyin da aka kulla na ayyukan kwangiloli wadanda aka shirya almundahana cikinsu da kuma karya ka'ida.

Kakakin shugaban kasar Khusela Diko, ya bayyana cewa, kammala wadannan batutuwa cikin sauri zai kara taimakawa hukumar SIU wajen gano wasu kudade ko kaddarorin gwamnati da aka yi sama da fadi da su ko kuma aka karkatar da su ba bisa ka'ida ba,.

Hakan yana tabbatar da cewa dukkan mutane dake da hannu wajen salwantar da kudade ko kaddarorin hukumomi za su kuka da kansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China