in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutane 128 da zargin aikata laifuka a lokacin zaben Najeriya
2019-02-25 10:08:33 cri

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce ta damke mutane 128 da ake zarginsu da laifukan ta da rikici a lokacin zaben shugaban kasa da na majalisun dokokin kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa Frank Mba ya bayyana cikin wata sanarwa cewa wadanda ake zargin an kama su ne daga dukkan sassan kasar wadanda ake tuhumarsu da laifukan da suka hada da yunkurin kisan kai, da sayen kuri'a, da satar akwati, da yin sojan gona, da kalaman batanci, da dai sauransu.

Ya ce an kwato makamai 38 da wasu abubuwan fashewa daga hannun mutanen a lokacin gudanar da zabukan, duk da cewa an samu fitar jama'a sosai kuma an gudanar zaben cikin kwanciyar hankali.

Kakakin hukumar 'yan sandan ya kara da cewa, babban sifeton 'yan sandan kasar ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike da sanya ido kan dukkan ayyukan masu tada rikici a lokacin zaben kasar kuma a kama dukkan wadanda ke da hannu wajen tada rikicin da kuma gurfanar da su a gaban shari'a.

Mba, ya kuma bayyana rashin jin dadinsa game da kalaman nuna kiyayya da neman ta da zaune tsaye da wasu ke yi da nufin tayar da hankalin jama'a, musamman wasu 'yan siyasa da magoya bayansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China