Daga cikin 'yan takarar da za su fafatawa a zaben har da shugaban kasar mai ci Macky Sall, da tsohon firaiministan kasar Idrissa Seck, da tsohon ministan harkokin wajen kasar Madicke Niang, da wani malamin jami'a Issa Fall, da kuma tsohon jami'in hukumar tattara hajarin kasar Ousmane Sonko. Ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Seck da shugaba mai ci Macky Sall. (Ahmad Fagam)