in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Venezuela ta yanke hulda da Colombia
2019-02-24 15:30:42 cri
Shugaban kasar Venezuelan Nicolas Maduro ya ayyana a jiya Asabar cewa kasarsa ta yanke duk wata huldar diflomasiyya da dangantakar siyasa a tsakaninta da makwabciyarta kasar Colombia, bayan da Colombian ta goyi bayan madugun adawar kasar Venezuelan da sojojin dake neman yiwa kasar mamaya.

"Na yanke shawawar yake duk wata huldar siyasa data diflomasiyya da gwamnatin kasar Colombia," Maduro ya fadawa taron gangamin magoya bayansa a birnin Caracas na kasar.

Jami'an diflomasiyyar kasar Colombia "tilas ne su fice daga kasarmu cikin sa'oi 24," injin Maduro.

Shugaban kasar Colombian Ivan Duque ya jaddada yin mubaya'arsa ga shugabancin madugun 'yan adawar kasar ta Venezuela kana ya kalubalaci gwamnatin mista Maduro. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China