An ji karar ababen fashewa da sanyin safiyar yau Asabar a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin Nijeriya, sa'o'i kafin fara kada kuri'a a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a kasar dake yamacin Afrika.
An ji karar fashewar abubuwan ne da misalin karfe 6 na safe a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Inda ake fama da ayyukan kungiyar Boko Haram.
Al'ummar Nijeriya sun fara kada kuri'a ne da misalin karfe 8 na safiya, a kusan rumfunan zabe 120,000 dake fadin kasar. An dage zaben ne da mako guda a kan lokacin da tun farko aka shirya gudanar da zaben.
Shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke neman zarce a wa'adi na biyu, ya kada kuri'arsa a mahaifarsa ta Daura, dake yankin arewacin kasar. (Fa'iza Mustapha)