in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gaggauta tattaunawar cinikayya tsakanin Sin da Amurka
2019-02-23 16:48:08 cri

Shugaban Amurka Donald Trump ya gana a jiya da Liu He, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firayin ministan kasar kuma jagoran bangaren kasar Sin kan tattaunawar tattalin arziki dake tsakaninta da Amurka, wanda ke tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jama'an kasashen biyu karo na 7 a birnin Washington na Amurka.

Shugaba Trump ya bayyana cewa, an riga an samu babban ci gaba yayin da ake gudanarwar tattaunawa a wannan karo, amma a sa'i daya kuma, akwai bukatar a ci gaba da kokari domin kammala sauran ayyuka, a don haka sassan biyu suka tsai da kudurin cewa, za su tsawaita lokacin tattaunawar har tsawon kwanaki biyu.

Wannan ne karo na farko da sassan biyu wato Sin da Amurka, suka tsai da kudurin tsawaita lokacin tattaunawar dake tsakaninsu tun bayan da suka fara, lamarin da ya nuna cewa, tattaunawarsu ta riga ta shiga mataki mafi muhimmanci bisa tushen samun babban ci gaba, haka kuma ya nuna cewa, tawagogin tattaunawar sassan biyu suna kara nuna kwazo da himma domin gaggauta tattaunawar, ta yadda za su tabbatar da burin da shugabannin kasashensu suka cimma.

Duk da cewa, ana samun ci gaban tattaunawar, dole ne a kara kokari. Tun bayan da Sin da Amurka suka fara gudanar da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu kasa da shekara guda da ta gabata, sassan biyu sun gamu da matsaloli daban daban, amma a karkashin jagorancin ra'ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, a karshe dai sassan biyu sun cimma matsaya guda kan wasu manyan batutuwa yayin da suka tattauna karo na shida a makon da ya gabata, haka kuma sun daddale wata yarjejeniyar fahimtar juna kan tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, lamarin da ya ciyar da tattaunawar gaba bisa babban mataki. Yanzu haka sassan biyu suna gudanar da tattaunawa karo na bakwai, tawagogin kasashen biyu sun samu nasarori da dama a fannonin daidaiton cinikayya da aikin gona da musayar fasahohi da kiyaye ikon mallakar fasaha da hidimar harkar kudi da sauransu.

Amma akwai wahala matuka idan ana son rubuta duk wadannan abubuwa, sassan biyu suna ganin cewa, ya zama wajibi su yi nazari sosai kan daukacin batutuwan da abin ya shafa, ta yadda za a rubuta su da kalmomin da suka dace, da haka za su kare moriyar kasashensu yadda ya kamata. A karkashin irin wannan yanayi, sassan biyu sun tsai da kuduri cewa, ya dace su tsawaita lokacin yin tattaunawar, da haka za su kara zurfafa cudanyar dake tsakaninsu, tare kuma da ciyar da tattaunawar gaba kamar yadda ake fata.

A sa'i daya kuma, an lura cewa, tsawaita lokacin yin tattaunawar shi ma ya nuna cewa, bayan kokarin da sassan biyu suka yi a cikin shekara guda daya da ta gabata, musamman ma tun bayan ganawar shugabannin kasashen biyu a kasar Argentina, suna fatan za su cimma matsaya guda a kan lokaci. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, Sin da Amurka suna dogaro ne da juna, idan suka hada kai, za su samu moriya tare, idan kuma ba haka, za su lalata moriyar juna, a don haka, gudanar da hadin gwiwar tsakaninsu zabi ne mafi kyau dake gabansu, kuma abubuwan da suka faru a cikin shekara daya da ta gabata sun riga sun shaida wannan lamari.

Bisa matsayinsu na manyan kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki a duniya, batun tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka yana da sarkakiya matuka, akwai wahala su cimma matsaya guda kan batun cikin kwanaki 90, amma dole ne a nace kan aikin. Yanzu sassan biyu suna ci gaba da gudanar da tattaunawa a tsakaninsu, shugaba Xi ya bayyana fatansa a cikin sakon da ya mikawa takwaransa na Amurka Trump, inda ya bayyana cewa, yana fatan sassan biyu za su sanya kokari tare domin daddale wata yarjejeniyar samun moriyar juna bisa tushen martaba juna da hada kai, shugaba Trump shi ma ya bayyana cewa, yana cike da imanin cewa, sassan biyu za su daddale wata yarjejeniya mai ma'ana wadda za ta amfane su duka, haka kuma yana sa ran cewa, zai sake ganawa da shugaba Xi ba da dadewa ba. Duk wadannan sun sa kaimi kan ci gaban tattaunawar matuka.

Kamar yadda aka sani, akwai bambance bambance da dama dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Amurka, misali yanayin da suke ciki da tsarin da suke amfani shi wajen gudanar da harkokin kasa da al'adun gargajiya da sauransu, shi ya sa kasar Sin ta fahimta sosai cewa, ba zai yiyu sassan biyu su warware rigingimun cikin sauki ba, amma tabbas kasar Sin za ta kara zurfafa yin gyare-gyare cikin gida da kara bude kofa ga kasashen waje, domin cimma burin samun ci gaban tattalin arziki mai inganci, saboda gudanar da harkokin kasa cikin lumana, aiki ne mafi muhimmanci na gwamnatin kasar Sin, haka kuma shi ne fasaha mafi daraja da gwamnatin kasar Sin ta samu a cikin shekaru 40 da suka gabata wato tun bayan da ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China