Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, ta ce za a tsare tare da gurfanar da duk wanda aka kama yana kada kuri'a kuma shekarunsa ba su kai ba, a babban zaben kasar.
Yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja babban birnin kasar, Shugban hukumar INEC Mahmood Yakubu ya bukaci a bada rahoton irin wadannan yara nan take, a duk inda aka gansu a fadin kasar.
Mahmood Yakubu, ya ce hukumar na aiki da 'yan sanda domin kama yaran da shekarunsu bai kai ba da masu daukar nauyinsu, yana mai cewa za a tsare duk wani yaro ya yi korin a tantance shi ko kuma kada kuri'a.
Ya kara da cewa 'yan Nijeriya da shekarunsu suka kai 18 ne kadai za su iya kada kuri'a a zabe.
Shugaban ya kuma shawarci al'ummar kasar da su sa ido kan duk wadanda suka yi kokarin tada rikici, yana mai bukatar a dauke su hoto ko bidiyo a aike shafin website na hukumar INEC.
Samun yara masu kada kuri'a abu ne da aka saba gani a arewacin kasar, kuma ya zama ruwan dare ne saboda akwai wasu dake daukar nauyinsu. (Fa'iza Mustapha)