in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gabanin zabe a Nijeriya, an gano wurare 12 da ka iya fuskantar barkewar rikici a kasar
2019-02-23 16:24:56 cri
Cibiyar bincike da bada bayanai game da rikice-rikice ta Nijeriya wato CCC, ta yi gargadi game da wuraren da ka iya fuskantar rikici a kasar, yayin da kasar ke tunkarar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.

A cikin rahotonsa na tsakiyar wannan wata, na tattarawa da yada bayanai game da yanayin rikice-rikice a fadin kasar, cibiyar ta gano wuraren da kai ya fuskantar barazanar tsaro a shiyyoyi 6 na kasar.

Shugban cibiyar Yusuf Anas, ya ce an gano wuraren ne bayan bitar al'amuran da suka faru a baya-bayan nan a wasu jihohi.

Jihohin da cibiyar ta bayyana sun hada da Kano da Kaduna da Kwara da Kogi da Adamawa da Taraba a shiyyar arewaci, sai kuma Lagos da Ogun da Rivers da Akwa Ibom da Anambra da Imo a shiyyar kudancin kasar.

Yusuf Anas ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da shugabannin al'umma da su shawarci mabiyansu game da kauracewa shiga duk wani abu da ka iya haddasa rikici da zai yi mummunan tasiri ga tsarin zaben. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China