in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana adawa da sanya sojoji don shiga tsakani a batun Venezuela
2019-02-22 19:51:41 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasarsa na adawa da shiga tsakani na soja da duk wani mataki da zai kai ga zaman dar-dar ko ma hargitsi a kasar Venezuela.

Jami'in ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani a taron manema labarai kan rahotannin dake cewa, Amurka za ta goyi bayan jagoran 'yan adawar kasar ya mika kayayyakin agajin jin kai cikin kasar a gobe Asabar.

Wasu masu sharhi sun yi imanin cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne domin haifar da tashin hankali da ma baiwa sojoji wata dama ta shiga tsakani.

Geng ya ce, gwamnatin Venezuela ta nuna hakuri tare da kai zuciya nesa, don hana aukuwar duk wani tashin hankali. Ya ce, idan har aka shigar da kayayyakin agajin da Amurka ke batu cikin kasar da karfin tuwo, kana tashin hankali ya barke, hakika sakamakon da hakan zai haifar ba zai yi kyau ba, kuma wannan ba abu ne da kowa zai so gani ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China