in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a takardun lamunin kasashen dake shawarar ziri daya da hanya daya ya kai kaso 8.1 a watan Janairu
2019-02-21 21:09:52 cri

Alkaluman ma'aikatar cinikayyar kasar Sin da aka fitar na nuna cewa, jarin da kasar ta zuba kai tsaye a takardun lamunin kasashe 47 dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya ya karu da kaso 8.1 cikin 100 a wannan shekara bisa makamancin lokaci na bara, adadin ya kai dala biliyan 1.33 a watan Janairun wannan shekara.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fiyar na cewa, jarin da kasar ta zuba a bangaren da bai shafi harkokin kudi ba cikin kamfanoni 973 dake kasashen waje a kasashe da yankuna 132 a watan da ya gabata ya kai dala biliyan 9.19 .

Kakakin ma'aikatar Gao Feng ya shaidawa taron manema labarai cewa, baki daya, alkaluman jarin kasar a wannan fanni a watan na Janairu, ya samu riba da kuma inganci, koda yake girman sa ya ragu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China