Geng Shuang ya bayyana hakan ne, lokacin da aka tambaye shi yayin taron manema labarai na yau, game da kalaman wasu kasashe dake cewa, wai ya kamata a cire kamfanonin ksar Sin daga aikin gina fasahar nan ta 5G, saboda"barazanar tsaro" kan kayayyaki da hidimar da kasar ke samarwa.
Jami'in na kasar Sin ya bayyana gabannin taron wayoyin sadarwa na duniya na 2019 da zai gudana daga ranar 25 zuwa 28 ga wata a birnin Barcelona na kasar Sfaniya cewa, fasahar 5G ba ta takaita ga kasa guda ko wasu kasashe kalilan ba, amma batu ne na ci gaban tattalin arzikin duniya, da muradun dukkan kasashe da ma ci gaban wayewar kan dan-Adam
Ya kara da cewa, rukunin kamfanonin duniya, da tsarin samarwa da ma adadin fasahar ta 5G a hade suke, kuma babu wanda zai iya raba su ko canja akalarsu, ko kuma ya shafi moriyar juna da hadin gwiwar moriyar juna ta kasa da kasa, wanda hakan ya saba yanayin kasuwa cikin adalci, da kassara dokokin kasa da kasa a fannin daidaito da nuna adalci da rashin nuna wariya.(Ibrahim)