Shugabannin sun bayyana haka ne a yayin tattaunawar da suka yi a Helsinki, babban birnin kasar Finland.
A cikin hadaddiyar sanarwar da aka fitar bayan tattaunawar, shugabannin shida sun bayyana cewa, abin da ya fi muhimmanci a gaban duniyar baki daya, shi ne ingiza "tsarin kasa da kasa dake bisa tushen dokoki, da ra'ayin kasancewar bangarori da dama mai amfani", kana sun sake nanata alkawarin da suka dauka na kiyaye amfani da ka'idojin kungiyar WTO.
Baya ga haka, shugabannin shida sun kalubalanci daukar manufar dake shafar kasar Sin bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da kyautata dangantakar dake tsakanin kawancen kasashen Turai da Amurka a fannonin cinikayya da zuba jari, da kuma bunkasa dangantakar dake tsakanin su da kasashen Afirka ta hanyar mafi dacewa. Kana sanarwar ta jadadda cewa, ya kamata kawancen kasashen Turai ya zama mai jagorancin duniya wajen tinkarar sauyin yanayi. (Bilkisu)