Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Sebastian Kurz, firaministan kasar Austria, wanda ke ziyara a kasar Amurka, inda shugaba Trump ya ce, ganawarsa da Kim Jong-un ta wannan karo ba zata zama ta karshe ba. A cewarsa, zai iya soke takunkumin da aka sakawa Koriya ta Arewa, sai dai ana bukatar kasar ta dauki wasu matakai " masu ma'ana". (Bello Wang)