in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaduwar makamai babbar barazana ce ga zaman lafiyar Afrika
2019-02-21 10:24:28 cri

Yaduwar kananan makamai ya kasance wata babbar barazana ga zaman lafiyar Afrika, Einas Mohammed, shugabar sashen kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar Afrika (AU), ta bayyana hakan a jiya Laraba.

Einas, ta bayyana hakan ne a lokacin bude taron karawa juna sani da kuma nazari kan tsara dabarun dakile yaduwar makamai wanda aka gudanar a Gross Barmen, kusa da babban birnin kasar Namibia, Windhoek.

Kananan makamai sun kasance a matsayin wasu kayayyaki na matakin farko da ake amfani da su wajen haddasa tashe tashen hankula bisa ga tarihin rikice rikice na Afrika, in ji ta.

Ta ce, a yayin tashe tashen hankula, kananan makamai suna haddasa laifuka masu yawa na take hakkin dan adam da dokokin samar da ayyukan jin kan al'umma wadanda suka hada da kisan kiyashi, da tilaswa mutane kauracewa muhallansu, da cin zarafin mata da kuma kaddamar da hare hare kan jami'an kiyaye zaman lafiya da ma'aikatan ayyukan jin kai. Haka zalika, barazanar kananan makamai ba ta tsaya ga tayar da hankali kadai ba. Matsalar ta shafi hatta tsaron kasa da lafiyar al'umma, har ma da sha'anin shugabanci baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China