in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Sin ya gana da ministan harkokin wajen Djibouti
2019-02-20 20:44:57 cri

A yau ne mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf, inda ya lashi takwabin karfafa musayar kwarewar harkokin shugabanci da kasarsa

Wang ya yi kira ga kasashen biyu, da su yi amfani da wannan dama wajen kara zurfafa alaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, bisa jagorancin shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) da ya gudana a shekarar da ta gabata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Da ya juya ga ci gaban da kasar Sin ta samu kuwa, Wang ya ce kasar Sin tana bin turbar tsarin gurguzu mai sigar musamman ne, inda take bin ka'idojin jam'iyya sau da kafa wajen tafiyar da harkokin kasa, da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da kara bude kofa ga kasashen waje, matakan da suka taimaka mata wajen biyan bukatan rayuwar al'ummarta.

A nasa jawabi, Youssouf ya ce, Djibouti ta gamsu da ci gaban akala bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninta da kasar Sin, kana ta yaba da taimakon da ta dade tana baiwa kasarsa. Ministan ya kara da cewa, a shirye Djibouti ta ke ta yi koyi da dabarun kasar Sin na samun ci gaba da yadda za ta raya jam'iyya mai mulkin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China