in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana kokarin yaki da cinikin dabbobi da tsirran dake bakin karewa
2019-02-20 19:45:25 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Laraba yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin yaki da laifuffukan dake shafar cinikin dabbobi da tsirran dake bakin karewa da kayayyakin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da dabbobin da tsirran ba bisa ka'ida ba, haka kuma tana gurfanar da masu aikata laifuffukan dake da nasaba da cinikin a kan lokaci.

Rahotanni na cewa, a kwanan baya kotun kasar Tanzaniya ta yankewa 'yar kasuwar kasar Sin mai suna Yang Fenglan hukuncin daurin shekaru 15 a gidan kurkuku bisa zarginta da laifin cinikin hauren giwa da nauyinsa ya kai kilo 1000.

Kan batun, Geng Shuang ya bayyana cewa, tun daga farkon shekarar 2015, kasar Sin ta dauki matakai a jere domin hana shigo da kayayyakin haurin giwar da aka sassaka cikin kasar, da hana farautar giwa da kuma daina sayar da kayayyakin haurin giwa, matakan da suka samu yabo daga wajen kasashen duniya baki daya. Har kullum gwamnatin kasar Sin ta bukaci daukacin 'yan kasarta dake kasashen ketare da su martaba dokokin kasashen da suke zaune a ciki, haka kuma kasar Sin tana goyon bayan hukumar da abin ya shafa ta kasar Tanzaniya kan matakin da ta dauka bisa doka, kana kasar Sin tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya domin ci gaba da kare dabbobi da tsirrai dake bakin karewa ta hanyar haramta cinikinsu ba bisa ka'ida ba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China