in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin: Ya kamata kasashen duniya su kara taimakawa Burundi
2019-02-20 19:32:10 cri

Jiya Talata mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su kara samar da taimakon jin kai da goyon bayan tattalin arziki ga kasar Burundi, kana ya jaddada cewa, ya kamata kwamitin sulhun MDD ya saurari ra'ayin kasar, ta yadda zai samar mata da taimakon da ya dace

Jami'in ya fadi hakan ne a yayin taron bainar jama'a da kwamitin sulhun ya kira game da kasar Burundi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, 'yan gudun hijirar Burundi da yawan gaske sun komo kasar daga kasashen waje sannu a hankali, kuma adadinsu zai karu cikin sauri a shekarar bana wato 2019 da muke ciki, a don haka kasar Sin tana fatan kasashen duniya su samar musu da taimako da suka dace a kan lokaci, ta yadda gwamnatin kasar Burundi za ta tsugunar da 'yan gudun hijirar yadda ya kamata.

Wu Haitao ya kara da cewa, kamata ya yi kasashen duniya su yaba da kokarin da gwamnatin Burundi ke yi wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, haka kuma su martaba 'yanci da hadin kan kasar da ma cikakkun yankunanta, tare kuma da martaba 'yancin gwamnati na tafiyar da harkokin kasa

Jami'in ya ci gaba da cewa, har kullum kasar Sin tana goyon bayan yunkurin Burundi na shimfida zaman lafiya, kuma tana son taka rawa domin cimma burin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma samun dauwamammen ci gaba a kasar ta Burundi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China