Trump wanda ya bayyana hakan ga 'yan jaridu, inda ya ce yana duba yiwuwar ganawa da Kim Jong Un, shugaban kasar Koriya ta arewa (DPRK), a mako mai zuwa a birnin Hanoi na kasar Vietnam. "Ina tunanin abubuwa masu yawa za su biyo bayan taron," in ji shi.
Shugaban na Amurka ya ce, yana son a kai wani muhimmin mataki game da shirin kawar da makaman nukiliyar na DPRK, amma sai dai ya ce ba gaggawa yake ba, tun da har yanzu takunkuman dake kan Pyongyang suna nan daram har sai lokacin da kasar ta dakatar da dukkan shirinta na kerawa da gwajin makaman nukiliyar.(Ahmad Fagam)