Yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan Yemen, Ma Zhaoxu ya ce ya kamata a ingiza bangarorin kasar zuwa ga cimma sulhu da yarjejeniyar siyasa mai dorewa, yana mai cewa ya kamata kuma su dage wajen ganin an bi ka'idojin MDD.
Wakilin na kasar Sin ya ce, suna fatan karkashin shugabancin kwamitin kula da tsagaita bude wuta a kasar, za a ga kyakkyawan kudurin shugabanci a aikace.
Ya ce suna fatan ganin an kaddamar da sabon zagayen tattaunawar zaman lafiya da wuri, bisa jagorancin manzon mussamam Martin Griffiths, ta yadda za a cimma sulhun da zai lura da bukatun dukkan bangarori tare da taimakawa wajen farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yemen. (Fa'iza Mustapha)