Sanya takunkumin na bangare guda ya sabawa 'yancin ikon kasa da dokokin kasa da kasa, kuma duk wani yunkuri na aza takunkumi kan wata kasa mai cin gashin kanta dole ne ya dace da dokokin yarjejeniyar MDD, inji Tijjani Muhammad-Bande, wakilin dindindin na Najeriya a MDD, wanda ya bayyana hakan a lokacin taron kwamitin musamman dake nazari kan yarjejeniyar dokokin MDD da kuma duba yadda za'a karfafa ayyukan hukumar.
Galibin takunkuman da aka sanyawa kasashe masu tasowa sun shafi kasashe mambobin kungiyar taryyar Afrika ne, da kungiyar kasashe 77 da kasar Sin, da kuma kungiyar kasashe 'yan ba uwanmu, in ji shi.
"Dole ne a rage karfin sanya takunkumin bangare daya, kuma a takaita wa'adin da ake dauka domin gujewa haifar da illa ga moriyar kasashen da abin ya shafa, da kuma al'ummomin kasashen," inji Bande.(Ahmad Fagam)