in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ci gaban yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau zai ingiza ci gaban duniya
2019-02-19 19:54:40 cri

A jiya Litinin ne kasar Sin ta fitar da wani shiri na raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ko kuma Greater Bay Area a turance, inda aka nuna wa kasashen duniya jadawali da taswirar gina yankunan bakin teku dake kumshe biranen da dama a nan kasar Sin wadanda ke sahun gaba a fadin duniya. An lura cewa, idan aka kwatanta da sauran yankunan dake bakin teku na kasashen duniya, yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau na kasar Sin suna da tsari na musamman, lamarin da ya nuna cewa, ya dace mahukuntan yankunan su kara yin kokari wajen yin kirkire-kirkire yayin da kasar Sin ke ci gaba da aiwatar da manufar yin gyaren fuska a gida da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za su cimma burin raya yankunan har su kasance abin koyi ga sauran yankuna a fadin kasar Sin.

A cikin shirin raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau da aka fitar jiya, an gabatar da burin da ake fatan cimmawa, wato za a gina yankunan dake kumshe birane da dama masu cike da kuzari wadanda za su kai matsayin koli a duniya, da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha ta kasa da kasa wadda za ta yi tasiri ga sauran kasashen duniya, da muhimman yankunan da za su taka babbar rawa yayin da ake aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, da yankunan gwaji wajen gudanar da hadin gwiwa mai zurfi tsakanin babban yankin kasar Sin da Hong Kong da Macau, da kuma yankuna masu inganci a fannonin rayuwa da aiki da kuma yawon shakatawa.

Fadin yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ya kai muraba'in kilomita dubu 56, adadin mutanen dake rayuwa a yankunan ya kai kusan miliyan 70 ya zuwa karshen shekarar 2017, alkaluman tattalin arziki wato GDP na yankunan ya kai kudin Sin yuan biliyan 10000. Duk da cewa fadinsu bai kai kaso 0.6 bisa dari ba cikin daukacin yankunan fadin kasar Sin, haka kuma adadin mutanen dake rayuwa a yankunan bai kai kaso 5 bisa dari ba cikin daukacin al'ummonin kasar, amma adadin GDP na yankunan ya zarta kaso 12 bisa dari na GDPn kasar, kana yankunan sun kasance yankunan dake kan gaba wajen bude kofa ga kasashen waje da kuma ci gaban tattalin arziki.

Idan aka kwatanta yankunan da sauran shahararrun yankuna masu ci gaba a fadin duniya, kamar su yankin tafiyar da harkar kudi na New York da yankin kimiyya da fasaha na San Francisco na kasar Amurka da yankin masana'antu na Tokyo a kasar Japan, yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau sabbin yankuna ne, amma suna da nasu fiffiko. Kwanan baya cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al'umma ta kasar Sin ta fitar da wani rahoton game da tasirin da wadannan yankuna hudu wato New York da San Francisco da Tokyo da kuma Guangdong-Hong Kong-Macau suke yi wa kasashen duniya, inda aka bayyana cewa, cikakken karfin tasiri na yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ya kai matsayi na uku, abu mai faranta rai shi ne, karfin tasirin tattalin arzikin su ya kai matsayin koli, saurin ci gaban tattalin arzikin yankunan ya ninka na sauran yankuna uku sauri har sau biyu.

Ban da haka, yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau suna da fiffikonsu a bayyane, misali, adadin cinikayyar shigi da ficin su ya ninka na yankin Tokyo har sau 3, adadin manyan akwatunan zuba kayayyakin da ake jigilar su a tasoshin yankunan ya ninka na daukacin sauran yankunan uku har sau ninki 4.5. Hakazalika, yankunan sun kunshi birane tara na lardin Guangdong da yankunan musamman na kasar Sin guda biyu wato Hong Kong da Macau, inda ake gudanar da yankunan da tsari iri biyu da yankunan harajin kwastam guda uku da kuma kudade iri uku a cikin kasa guda daya.

Domin cimma burin raya yankunan lami lafiya, shirin raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ya gabatar da manufa a fannoni shida wato yin kirkire-kirkire yayin yin kwaskwarima, da raya yankunan bisa tushen yin hadin gwiwa, da raya yankunan tare da kiyaye muhalli, da yin hadin gwiwa ba tare da rufa rufa ba domin samun moriya tare, da cin gajiyar sakamakon ci gaban yankunan domin kyautata rayuwar al'ummar yankunan, da kuma gudanar da kasa daya bisa tsari da doka. Ko shakka babu za a raya yankunan ta hanyar kara yin kirkire-kirkire da gyaren fuska da kuma bude kofa ga kasashen waje. Haka kuma tabbas ne ci gaban yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, haka kuma zai ingiza ci gaban tattalin arzikin kasashen duniya baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China