in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta fitar da wani shirin raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau
2019-02-19 14:11:36 cri

A jiya Litinin ne kasar Sin ta fitar da wani shiri na raya yankunan Guangdong-Hong Kong-Macau ko kuma Greater Bay Area a turance, yankuna ne masu karfin tattalin arziki kuma kofarsu a bude take ga kasashen duniya. Bisa shirin, gwamnatin kasar Sin na fatan gina yanki na musamman da zai kunshi tsarin birane na zamani, wanda zai kara bada goyon-baya da jagoranci ga ci gaban tattalin arziki gami da bude kofar kasar ga kasashen ketare.

Bisa wannan gagarumin shiri, yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau na kunshe da yankin musamman na Hong Kong, da na Macau, gami da wasu birane guda tara dake lardin Guangdong, ciki har da Guangzhou, da Shenzhen, da Zhuhai da Foshan. Fadin wannan yanki na musamman ya kai murabba'in kilomita dubu 56, wanda ke kunshe da mutane kimanin miliyan saba'in.

Alkaluma sun nuna cewa, duk da cewa fadin yankin na musamman bai kai kashi daya bisa dari na fadin duk yankin kasar Sin ba, kuma yawan mutanen yankin bai kai kashi biyar bisa dari na yawan al'ummar kasar Sin ba, tattalin arzikinsa ya kai kashi 12 bisa dari na yawan GDP na duka kasar baki daya. Kwararru da masana na ganin cewa, raya wannan yanki na Guangdong-Hong Kong-Macau na da matukar ma'ana ga ci gaban duk kasar baki daya. Babban sakatare na cibiyar nazarin yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau Deng Jiangnian ya bayyana cewa:

"Yawan GDP na yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau ya kai kudin Sin RMB triliyan goma, wanda ke kunshe da tsarin masana'antu 270 da kasuwannin musamman 330, abun da ya samar da babban zarafi ga sauya fasahohin kere-kere don su zama masu karfin tattalin arziki."

Wannan shirin da aka fitar, na raya yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau na maida hankali sosai kan yin kirkire-kirkire da tsare-tsare, inda aka bayyana cewa, ya kamata a kara musanya albarkatu, da daukar matakai daban-daban don inganta karfin yin kirkire-kirkire da raya kasuwanni da dama. A nasa bangaren, wani masani a fannin tattalin arziki da fasahohi daga cibiyar nazarin harkokin zamantakewar al'umma ta kasar Sin, Li Ping ya bayyana cewa:

"Yankunan Guangdong da Hong Kong da kuma Macau, suna da mabambanta tsare-tsare. Yaya za'a yi a kawar da bambance-bambancen? Yaya za'a yi a cire shingen dake tsakaninsu, ta yadda za'a samar da sauki ga musayar mutane da kayayyaki da kudade ba tare da matsala ba? Wannan shi ne babban batun da muke mai da hankali a kai. Raya tattalin arziki bisa bukatun kasuwanni na bukatar musayar albarkatu iri-iri cikin sauki, ta yadda za'a kara samun karfin yin takara."

Wasu mutane daga bangarorin kere-kere, da sadarwa da kuma kasuwanci da masana'antu na ganin cewa, yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau na da cikakken tsarin masana'antu da goyon-bayan kudade sosai, har ma yana da babban karfin yin kirkire-kirkire. A nasa bangaren, shugaban dandalin tattaunawa mai suna Wisdom Hong Kong, Wu Lishan, ya nuna cewa:

"Yankin Hong Kong na da kyawawan manufofin kudi da yin kirkire-kirkiren fasaha da kuma kwararru, haka kuma babban yankin kasar Sin na da albarkatu masu tarin yawa wanda ke bunkasuwa cikin sauri, don haka bangarorin biyu na iya yin hadin-gwiwa sosai."

A nan gaba kuma, yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau zai ci gaba da kyautata yanayin zuba jari da kasuwanci a wasu birane tara dake lardin Guangdong, da gaggauta bude kofa ga kasashen waje don habaka tattalin arzikin wurin. Mataimakin shugaban kungiyar nazarin tattalin arziki na yankuna ta kasar Sin, Chen Yao ya nuna cewa:

"A wani bangaren, ya kamata Hong Kong da Macau su shiga cikin babban shirin raya kasa gaba daya, da hada kai tare da babban yankin kasar Sin don yin takara tsakanin kasa da kasa, musamman a fannin aiwatar da shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Alal misali, Hong Kong ita ce cibiyar tattalin arzikin duniya, inda ake samar da kyawawan hidimomi a fannonin kudade da zirga-zirgar jiragen ruwa da cinikayya da dokoki da makamantansu."(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China