in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Niger: Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 6
2019-02-19 11:08:57 cri
Hukumar tsaro ta jamhuriyar Nijar ta sanar a jiya cewa, 'yan kungiyar Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake a wani wurin karbar 'yan gudun hijira dake jihar Diffa ta kasar a ranar Lahadin da ta gabata, inda mata 2 suka ta da nakiyar dake jikunansu, tare da kashe kansu, gami da 'yan gudun hijira 3, da wani mazaunin wurin.

Kasancewar jihar Diffa dab da kan iyakar kasashen Nijar da Najeriya, ya sa ake ganin hare-hare masu yawa da 'yan ta'adda na kungiyar Boko Haram suke kai wa wurin, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da yawa a shekarun nan.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China