A baya, an shirya cewa, taron zai gudana ne a jiya Litinin zuwa yau Talata, inda zai samu halartar kasashe mambobin kungiyar Visegrad da suka hada da Poland da Hungary da Jamhuriyar Czech da kuma Slovakia.
An fasa taron ne bayan sabon mukaddashin ministan harkokin wajen Isra'ila Yisrael Katz ya bayyana a ranar Lahadi cewa, jama'ar Poland sun hada hannu da 'yan Nazi yayin yakin duniya na II.
Da safiyar jiyan ne Jakadan Poland a Isra'ila Marek Morawiecki, ya bayyana tsokacin a matsayin abun kunya da kuma wariyar launin fata.
Daga baya kuma, Firaministan Poland din Mateusz Morawiecki ya soki tsokaci sannan ya sokewa ministan harkokin wajen kasarsa halartar taron.
Bayan Poland ta janye daga taron ne kuma Jamhuriyar Czech ta sanar da soke taron.
Tuni dai Firaministan Hungary Viktor Orban da na Slovakia Peter Pellegrini suka isa Isra'ila, inda kuma ake sa ran isar Firaministan kasar Czech Andrej Babis.
A cewar Ministan harkokin wajen Isra'ila, Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, zai gana da shugabannin daya bayan daya, game da dangatakar dake tsakanin kasashensu. (Fa'iza Msutapha)