in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a bude gasar samun kyautar Jack Ma ga masu sana'o'i a Afrika
2019-02-19 10:15:52 cri
Mai kamfanin Alibaba na kasar Sin, Jack Ma, ya kaddamar da wani asusu a jiya, da nufin samar da dala miliyan 10 ga hazikan 'yan Afrika masu sana'o'i cikin shekaru 10 masu zuwa.

A cewar gidauniyar Jack Ma, za a bada kyautar ne ga 'yan Afrika 10 masu sana'o'i, inda a kowacce shekara za a bada dala miliyan 1.

Za a bude shiga gasar cin kyautar ga dukkan 'yan Afrika ne a ranar 27 ga watan Maris, inda ake sa ran yin gasa ta karshe a nahiyar cikin watan Nuwamba.

Gidauniyar na da nufin karfafawa hazikan 'yan Afirka 100 masu sana'a gwiwa ya zuwa 2030, domin taimakawa nahiyar.

A watan Augustan bara ne Shugaban kamfanin na Alibaba, ya sanar da kafa wani asusu da zai karfafawa 'yan Afrika gwiwar cin gajiya daga tsarin tattalin arziki na zamani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China