in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya yi gargadin daukar hukunci mai tsanani kan masu aikata magudin zabe
2019-02-19 09:50:23 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa sojoji da 'yan sandan kasar umarnin daukar tsauraran matakai kan dukkan wadanda aka samu da hannu wajen aikata magudin zabe, kamar satar akwati, wanda hakan zai iya kawo cikas ga manyan zabukan kasar da aka dage.

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da kusoshin jam'iyyar ta APC mai mulki a Abuja, ya ce duk wani dan siyasar da ya kuskura ya dauki nauyin 'yan daba domin hargitsa zaben kasar ko kuma satar akwati a lokacin zabukan, to ya kuka da kansa.

A ranar Asabar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, ta sanar da dage zabukan kasar inda ta kara wa'adin mako guda, bisa matsalolin da ta ce suna da nasaba da kayayyakin aikin zaben.

Shugaba Buhari, wanda ke neman wa'adin mulki na biyu a zaben shugaban kasar da aka dage, ya ce jami'an tsaron kasar sun riga sun fahimci wuraren da ake da fargabar tashin rikici, kuma tuni sun gano irin wadannan wuraren kuma za su dauki dukkan matakan da suka dace.

A cewar shugaban kasar, jami'an tsaron kasar a shirye suke su dauki kwararan matakai na dakile duk wasu laifukan zabe a lokacin zabukan da ma bayan zabukan kasar.

Tsaro shi ne batu mafi girma game da zaben Najeriya. Baya ga batun rikice rikice da ake samu a tsakanin magoya bayan jam'iyyun siyasa, akwai kuma dakarun tsaron kasar dake bakin daga domin yaki da mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China