in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta shirya bunkasa manufofin kafa yankin musamman
2019-02-18 20:04:02 cri

A yau ne kasar Sin ta fitar da wani shirin raya yankuna Guangdong-Hong Kong-Macao ko kuma Greater Bay area a turance. Bisa shirin, nan da shekarar 2022, gwamnati na fatan gina yanki na musamman da zai kunshi tsarin birane na zamani da fasahohin kirkire-kirkire da babu kamarsu a duniya. Sauran abubuwan sun hada da tsarin masana'antu da yanayin muhalli mai inganci.

Haka kuma,a karkashin shirin, akwai takarda ta musamman wanda ke yin jagora kan hadin gwiwa da ci gaban da ake samu a halin yanzu da ma nan gaba kan yankin na musamman, daga yanzu har zuwa shakarar 2022 na matsakaicin wa'adi daga bisani kuma a kara wa'adin shirin na dogon lokaci zuwa shekarar 2035.

Takardar ta kuma bayyana cewa, nan da shekarar 2022, karfin yankin zai karu, sannan ya kamata a kara karfafa tare da fadada hadin gwiwa tsakanin Guangdong, Hong Kong da Macao, aka kuma kara bunkasa matakan ci gaban yankin.

Sannan bisa tsarin, nan da shekarar 2035, ya kamata tsarin tattalin arziki da dabarun ci gaban yankin ya samu tallafin goyon bayan kirkire-kirkire, ta yadda karfinsa na tattalin arziki da fasahar kere-kere za ta kara bunkasa, kana gasarsa a bangaren kasa da kasa da ma tasirinsa su kara yin karfi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China