Bayanai da majalisar kula da harkokin masana'antun sarrafa kanannan kayayyaki ta kasar Sin, sun ce kudin shigar da bangaren ya samu ya kai kaso 6.2 yayin da ya samu ribar kaso 5.5.
Sai dai, bayannan sun nuna cewa, har yanzu alkaluman bangaren a cikin tattalin arzikin kasar bai kai matsakaicin mataki ba, wanda ke nuna cewa bangaren na samun koma baya saboda karuwar kudaden da ake kashewa da raguwar riba.
Majalisar na shirin daukar managartan ka'idojin sana'a a bangaren a bana, domin tabbatar da ya kai miznin na kasashen ketare.
Za a kara samar da nau'in sanao'in guda 15 masu mu'amala da juna yayin da za a samar da wasu na kare muhalli 3 da za a karfafa su. (Fa'iza Mustapha)