Zarif ya bayyana hakan ne a lokacin taron kasa da kasa kan sha'anin tsaro na Munich, ya ce, ya kamata kasashen Turai su kara kaimi muddin suna son kiyaye dangantakar su da Iran, ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen Turai su gabatar da tsarin tattaunawa na gamayyar hadin gwiwar kasa da kasa.
Kana Zarif ya ce, "Dole ne Turai su yi wani hobbasa muddin suna son kaucewa makircin Amurka na neman zaman zama saniyar ware," a cewarsa Iran a shirye take ta mutunta yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015, wacce aka cimma da manyan kasashen duniya.
Jawabin da Zarif ya gabatar, yazo ne kwana guda bayan da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya bukaci kasashen Jamus, Faransa, da Birtaniya dasu goyi bayan Amurka wajen janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar kana su daina neman kawo nakasu kan takunkuman da Amurkar da kakabawa Iran. (Ahmad)