in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron kasa da kasa kan sha'anin tsaro na Munich karo na 55
2019-02-18 11:14:45 cri
A jiya Lahadi aka kawo karshen taron tsaro na kasashen duniya na Munich karo na 55 (MSC), mafi yawa daga cikin mahalarta taron sun bayyana ra'ayoyinsu cewa dokokin kasa da kasa suna fuskantar mummunar barazana.

A jawabinsa na rufe taron, shugaban taron na MSC Wolfgang Ischinger, yace, a lokacin taron dandalin na kwanaki uku, an lura cewa dokokin kasa da kasa suna cikin wani mawuyacin yanayi.

Bisa ga yanayin sauye sauyen dokokin kasa da kasa, taron kolin MSC, wanda muhimmin taro ne na shekara na kasa da kasa wanda ke tabo batutuwa da suka shafi tsaro, ya samu mahalarta sama da 500, da suka hada da shugabannin kasashe da na hukumomin gwamnatoci da sauran kososhin hukumomin tsaro na kasa da kasa.

Ischinger ya lura cewa, rahoton taron MSC na 2018 ya bayyana cewa, duniya tana fuskantar tashe tashen hankula da rashin tabbas, ana cikin halin rashin tabbbas. Amma a wannan shekarar, taron na MSC ya yi tambaya cikin sabon rahotonsa cewa wanene za'a dorawa alhakin karya yarjejeniyar kasa da kasa, mahalartar da dama sun bayyana ra'ayoyinsu.

A taron MSC karo na 55, ya tattaro batutuwan tsaro na kasa da kasa, kamar su batun yin takara da hadin gwiwar manyan kasashe masu karfin fada aji, da makomar EU, da sauran batutuwan dangantaka da aka tattauna kansu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China