Ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan masu fama da talauci a kauyuka ya ragu zuwa miliyan 16.6 bisa miliyan 98.99 a karshen shekarar 2012, wato ya ragu da miliyan 82.39, sannan yawan sabbin masu fama da talauci ya ragu zuwa kashi 1.7 cikin dari bisa kashi 10.2 cikin dari na shekarar 2012, wato ya ragu da kashi 8.5 cikin dari.
Binciken ya nuna cewa, a shekarar 2018, matsakaicin yawan kudin shiga na ko wane mazaunin kauye a yankuna masu fama da talauci ya kai RMB yuan 10,371, wato ya karu da yuan 994. Wanda ke nufin kowanne mutum 1 ya samu karin kaso 10.6. amma saboda sauyawar farashin kayayyaki, karin ya tsaya ne kan kaso 8.3 cikin dari. Karuwar kudin shigar da mazauna kauyuka masu fama da talauci suka samu, ya fi na dukkan mazauna kauyukan dake fadin kasar Sin. (Bilkisu)