in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kubutar da mutane 80 da aka yi garkuwa da su a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya
2019-02-18 09:55:52 cri
Kimanin mutane 80 dakarun tsaron Najeriya suka kubutar daga hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da su a jahar Zamfara dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, wani jami'i ne ya bayyana hakan a ranar Asabar.

A wata sanarwa da aka fitar a Gusau, babban birnin jahar Zamfara, kakakin rundunar sojin saman Najeriya Clement Abiade ya sanar cewa, mutanen da aka yi garkuwa da su sun hada da maza, mata da kananan yara da suka fito daga wasu yankunan jahar ta Zamfara.

A makon da ya gabata ne, dakarun sojojin Najeriya suka kaddamar da samame babu kakkautawa inda suka yiwa 'yan bindigar kofar rago daga dukkan bangarori, hakan ya taimaka wajen karya lagon maharan, inji jami'in.

Kakakin rundunar sojojin ya ce an damke mutane 6, wadanda ake zargin barayin shanu ne, da masu yin garkuwa da mutane ne, da kuma wasu makamai, da alburusai har ma da wasu dabbobi da aka gano sun sace.

Wadanda aka damke din za'a mika su ga hukumar 'yan sanda domin gudanar da bincike da zartar musu da hukunci, inji Abiade.

Yankunan karkarar jahar Zamfara sun jima suna fuskantar hare haren 'yan bindiga, da barayin shanu, da masu yin garkuwa da mutane, inda aka samu wasu munanan hare hare biyu a watan Disambar 2018, wadanda suka yi sanadiyyar hallakar rayukan mutane masu yawa. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China