A ranar Alhamis ne Najeriya ta bada umarnin rufe dukkan iyakokinta domin samun nasarar gudanar da manyan zabukan kasar wanda a baya aka shirya gudanarwa ranar Asabar din da ta gabata.
A cikin wata gajeriyar sanarwa wanda babban kwantiloran hukumar shigi da fici na kasar, Muhammad Babandede, ya sanar, ya ce, an sake bude kan iyakokin kasar domin cigaba da zirga zirgar jama'a ta yau da kullum.
Babandede yace, jami'an hukumar shigi da ficin zasu cigaba da gudanar da ayyukansu na tsaron kan iyakokin kasar domin tabbatar da ganin dukkan wadanda ke shigi da fici ta hanyoyin kasa, sama, da ta ruwa suna da cikakku kuma ingantattun takardun da ake bukata.
Da sanyin safiyar ranar Asabar ne hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta sanar da dage manyan zabukan kasar inda ta kara mako guda, sakamakon wasu matsoli da suka sha kanta dake da alaka da kayan aiki. (Ahamd Fagam)