in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan Najeriya sun bayyana rashin jin dadi game da dage babban zaben kasar
2019-02-17 17:31:09 cri

A ranar Asabar din da ta gabata al'ummar Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu game da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta dauka na sauya ranakun gudanar da manyan zabukan kasar yayin da ya rage 'yan awowi gabanin a fara jefa kuri'a a duk fadin kasar domin zabar shugaban kasa da 'yan majalisun dokokin kasar.

Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben Najeriyar, ya bayyanawa manema labarai cewa, hukumar ta INEC ta dage zaben shugaban kasar wanda da farko ta shirya gudanarwa a ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, wannan mataki ya biyo bayan wasu matsaloli ne da suka sha kan hukumar. Haka zalika INEC ta dage zaben gwamnonin jahohi da na majalisun dokoki na jahohin kasar wadanda aka shirya gudanarwa a ranar 2 ga watan Maris zuwa karin mako guda.

Ko da yake wannan ba shi ne karo na farko da ake sauya ranakun gudanar da babban zabe a kasar ba, amma dage zaben na wannan karo ya janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar.

Kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulkin kasar ya ce, ya yi matukar bakin ciki da wannan matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na sauya ranakun zaben kamar yadda ta ayyana.

"Mun yi Allah wadai da wannan mataki na jinkiri da hukumar shirya zaben kasar ta dauka," jamiyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin jamiyyar ya fitar.

Ya ce, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya baiwa hukumar zaben cikakken hadin kan da take bukata domin tabbatar da shirya ingantaccen zabe tare da baiwa hukumar dukkan ababen da take bukata a kan lokaci.

"Muna fatan hukumar ta INEC za ta yi adalci ga kowane bangare a cikin dukkan harkokinta," in ji kakakin.

A nata bangaren, babbar jam'iyyar adawar kasar PDP ta yi Allah wadai da dage ranakun zabukan kasar, inda ta bayyana matakin da cewa "rashin kirki ne."

Cikin wata sanarwa, shugaban jam'iyyar PDP Uche Secondus ya ce, abin da hukumar zaben ta yi tamkar wasa ne da hankalin 'yan Najeriya na dage zabukan kasar.

Shugaban na PDP ya kara da cewa, jam'iyyarsu ba za ta amince da wannan rashin dattaku da hukumar zaben kasar ke aikatawa ba, kana ya gargadi hukumar ta guji aikata magudi, ko cin zarafin masu kada kuri'a da 'yan hamayya, musamman 'yayan jam'iyyar adawa ta PDPn.

Sama da 'yan Najeriya miliyan 84 ne suka yanki katin jefa kuri'a domin shiga zabukan wadanda aka dage lokacin gudanarwa.

Gabanin gudanar zabukan, jama'ar Najeriya suna ta dokin zuwa rumfunan zabe don jefa kuri'unsu a zabukan kasar mafi yawa jama'a a nahiyar Afrika. Zaben ya kuma ja hankalin al'ummar kasa da kasa, inda bangarori daban daban ke tofa albarkacin bakin kan batun.

Jama'a da dama 'yan kasar suna ci gaba da bayyana takaicinsu game da matakin da hukumar ta INEC ta dauka na dage zabukan kasar, galibin jama'a suna zargin hukumar da gazawa wajen sauke nauyin dake bisa wuyanta.

Masu ta'ammali da shafukan sada zumunta da dama suna yi ta kira kiraye ga shugaban hukumar zaben da ya yi murabus.

Olufunmilayo Odunaike, wani mai bibiyar shafin Facebook ya ce, ya kamata hukumar zaben kasar ta dauki wannan mataki ne tun a wasu makonnin da suka gabata idan har ta lura akwai matsala.

Temitope Adeboye, shi ma mai bibiyar shafin Facebook, ya bukaci a gudanar da binciken musabbin dage zaben.

Folorunsho Amsat, wata 'yar jarida, ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua daya daga cikin illolin da dage zaben zai iya haifarwa ga masu zaben musamman game da yiwuwar kashe gwiwar da dama daga cikin masu kada kuri'ar, wata kila matakin zai iya haifar da raguwar masu fitowar kada kuri'ar.

Sai dai a cewar babban jami'in hukumar ta INEC, dage zaben ya kasance wani mataki mai matukar wahala wanda da ya zama tilas hukumar ta dauka.

Sama da awoyi 7, shugaban hukumar zaben da manyan kwamishinonin hukumar ta INEC su 12 sun yi wata ganawar sirri a daren Juma'a.

Ana sa ran zaben zai gudana ne a rumfunan zabe 119,973 dake fadin kasar, kana da manyan cibiyoyin tattara sakamakon zaben kimanin 8,809 a fadin kananan hukumomi 774 dake fadin kasar da kuma birnin tarayya Abuja.

Wasu majiyoyi sun danganta dage lokacin zaben da cewa ba zai rasa nasaba da rashin kayyakin aikin zaben a wasu sassan kasar ba.

INEC ta ce, mataki da ta dauka na dage zaben zai ba ta cikakkiyar damar kammala dukkan shirye shiryen da suka dace don samun sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China