Rahotannin da aka ruwaito sun ce, a kwanakin baya ne ministan harkokin wajen Venezuela ya ce, wasu kasashe ciki har da kasar Sin na yunkurin kafa wasu kungiyoyi don marawa gwamnatin Maduro baya, wadanda kuma nan bada dadewa ba za su dauki matakai don sanya kasashen duniya fahimtar irin hadarin da jama'ar kasar Venezuela suke fuskanta. Game da wannan batu ne, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasarsa tana kira ga bangarori daban-daban da su goyi bayan dukkan jam'iyyun siyasar Venezuela, wajen lalubo bakin zaren daidaita rikicin kasar ta hanyar yin shawarwari cikin lumana. Kana kuma, Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su mutunta ka'idoji gami da manufofin kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, yana mai cewa bai kamata a rika tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen duniya ba. (Murtala Zhang)