in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren da aka kai wasu kauyukan Najeriya sun haddasa mutuwar mutane a kalla 66
2019-02-16 15:28:08 cri
An kai hare-hare kan wasu kauyuka 8 dake jihar Kadunan Najeriya a jiya Juma'a, inda 'yan sanda suka gano gawarwaki 66, ciki har da yara 22, yayin da aka garzaya da mutane 4 da suka ji raunuka zuwa asibiti. Rahotanni na cewa, zuwa yanzu, an riga an kama wasu da ake tuhuma da hannu cikin hare-haren, amma ba a sanar da sunaye da dalilinsu na kaddamar da hare-haren ba.

Da ma a yau Asabar aka shirya gudanar da babban zaben kasar, inda tun cikin watan Janairun bana, gwamnatin kasar ta gargadi tare da ambatar wasu wurare da rikici ka iya barkewa a lokacin zaben, ciki kuwa har da jihar Kaduna. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China