Bayanai na nuna cewa, jarin ketare na kai tsaye da aka zuba cikin kasar a shekarar da ta gabata, ya kai dala biliyan 15.36, yayin da jarin da kasar ta zuba kai tsaye a ketare ya kai dala biliyan 11.287.
Kana jarin takardun lamuni da hukumomin kudi na cikin gida suka zuba a shekarar 2018 ya kai dala biliyan 7.35. Baki daya ya zuwa karshen shekarar 2018, jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a hukumomin kudin cikin gida ya kai dala biliyan 143.122, yayin da jarin takardun lamunin hukumomin kudin cikin gida ya kai dala biliyan 251.771.(Ibrahim)