Kwanan baya mataimakin shugaban hukumar kula da injunan aikin gona da makiyaya ta jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin Gulnar Ubul ta rubuta wani rahoto, inda ta bayyana cewa, a cikin shekarun baya bayan nan, jihar Xinjiang tana kokarin daukan matakai domin magance aukuwar ayyukan ta'addanci, tare kuma da gudanar da aikin koyar da ilmin sana'a ga al'ummar yankin, makasudin aikin shi ne domin kubutar da su daga matsalar tsattsauren ra'ayi, tare kuma da kyautata rayuwarsu.(Jamila)