in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadaddiyar sanarwar Rasha da Turkiyya da Iran ta jaddada muhimmancin kiyaye ikon mulki da cikakken yanki na Syria
2019-02-15 10:13:21 cri

Jiya Alhamis shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da kuma shugaban kasar Iran Hassan Rouhani sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa a birnin Sochi dake kudancin Rasha, inda suka jaddada cewa, dole ne a kiyaye ikon mulki da cikakken yankin kasa na Syria.

Wadannan shugabannin kasashe uku wato Rasha da Turkiyya da Iran, sun yi tattaunawa tsakaninsu game da yanayin siyasa da Syria ke ciki da kudurin da Amurka ta zartas na janye sojojinta daga kasar ta Syria da sauransu. A cikin hadaddiyar sanarwar da suka fitar bayan tattaunawar, shugabannin uku sun bayyana cewa, kasashensu za su ci gaba da nacewa ga manufar kiyaye ikon mulkin kasa da 'yancin kai da dunkulewa waje guda da cikakken yankin kasa a kasar ta Syria, haka kuma za su ci gaba da martaba muradu da ka'idojin MDD. Kana kasashen uku suna ganin cewa, ya dace daukacin kasashen duniya su martaba duk wadannan ka'idojin, bai kamata ba a take su.

Hadaddiyar sanarwar ta bayyana cewa, kasashen Rasha da Turkiyya da Iran ba za su amince a daukar sabbin matakai kan Syria bisa kafa hujja da yaki da ta'addanci ba, kuma ba za su amince da shirin kawo baraka ga Syria da za a aiwatar da shi bisa makarkashiyyar lalata ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasa da tsaron kasashe makwabtaka na kasar Syria ba. Idan Amurka ta cika alkawarinta na janye sojoji daga Syria, to lamarin zai taimaka wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasar ta Syria.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China