in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump zai sanya hannu kan bukatar neman kudade da ayyana bukatar gaggawa
2019-02-15 09:59:02 cri

Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana shirin sanya hannu kan kudurori biyu kan batun neman kudi da kuma tsaron kan iyakar kasar domin gujewa fuskantar sake rufe ma'aikatun gwamnatin kasar, amma ya sake ayyana bukatar gaggawa na neman kudade don cika alkawarin da ya jima da yi na gina katanga a iyakar kasar, fadar White House ne ta sanar a jiya Alhamis.

"Shugaba Trump zai sanya hannu kan kudurin neman kudade na gwamnati, kamar yadda ya ambata tun a baya, zai kuma dauki wasu matakai wadanda suka hada da sanya dokar ta baci domin tabbatar da tsaron kasar da daidai yanayin da al'umma ke ciki a kan iyakokin kasar." kakakin fadar ta White House Sarah Sanders ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.

"Shugaban kasa yana son cika alkawarin da ya dauka na gina katanga, da tsaro kan iyakar kasa, da kuma tabbatar da samarwa kasarmu kariya," in ji ta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China