Rahotannin na cewa, a jiya Laraba, shugaban kasar El-Salvador Nayib Bukele ya zanta da mai taimakawa shugaban Amurka kan harkokin tsaro John Robert Bolton ta waya, inda ya ce El-Salvador babbar aminiyar Amurka ce. A nasa bangare Bolton ya ce, bangarorin biyu sun tattauna ne kan yadda za su karfafa zumuncin dake taakaninsu da yakar ayyukan kwace albarkatun da kasar Sin take yi a bangaren duniyarmu daga yamma.
Game da hakan, Madam Hua ta jaddada cewa, sam kasarta ba ta da niyyar yin takara a yankin Latin Amurka. Kuma hadin-gwiwar da kasar Sin take yi da kasashen Latin Amurka, ciki har da El-Salvador, hadin-gwiwa ce dake kawowa juna moriya, da nufin samun ci gaba kafada da kafada, al'amarin da ya kara inganta hadin-gwiwarsu.(Murtala Zhang)