in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin wajen Sin: Ya kamata a mutunta gaskiya kan batun tsaro
2019-02-14 20:02:41 cri
Rahotannin da aka ruwaito na cewa, wani tsohon babban jami'in babbar hedikwatar harkokin sadarwar leken asiri ta gwamnatin Birtaniya ko kuma GCHQ a takaice, Robert Hannigan, ya wallafa wani bayani a jaridar Financial Times inda ya bayyana cewa, kawo yanzu ba'a gano wata shaida da ta nuna cewa, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wasu munanan ayyukan Intanet da ba su dace ba ta hanyar amfani da kamfanin kasar wato Huawei, kana ya ce, bai kamata kasashen yammacin duniya su ki amincewa da na'urori da hidimomin da kasar Sin mai karfin kimiyya da fasaha take samarwa ba.

Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a yau Alhamis cewa, ya zama dole a mutunta gaskiya idan aka ambaci maganar tsaro. Kasar Sin na fatan bangarori daban-daban za su mutunta ka'idojin kasuwanni na yin takara cikin adalci kuma ba tare da kafa wani shinge ba, da samar da wani yanayin kasuwanci mai kyau ga hadin-gwiwar kamfanoni daban-daban ba tare da nuna wani bambanci ba, ta yadda za a raya sana'o'i ta hanyar da ta dace.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China