in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin ya jaddada muhimmancin warware rikin Iraqi ta hanyar siyasa
2019-02-14 10:54:35 cri
Wakilin kasar Sin ya jaddada muhimmancin yin amfani da matakai na siyasa wajen warware matsolin da suka shafi kasar Iraki a lokacin da jami'in na Sin ke jawabi ga kwamitin sulhun MDD game da halin da ake ciki a Irakin.

"Tabbatar da nasarar cimma daidaito da samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin bangarorin kasar Iraki ya dace da manufar ci gaba kuma shi ne babban muradin al'ummar kasar Iraki," Ma Zhaoxu, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, shi ne ya bayyana hakan a lokacin taron.

Ya kara da cewa, Iraqi tana cikin wani muhimmin mataki na bukatar ingiza zaman lafiya, da tsaro, da sake gina kasa, wakilin na Sin ya bukaci al'ummar kasa da kasa da su mutunta 'yancin kasar Iraki na ikon mallakar kasarta, da kasancewarta kasa mai cin gashin kai, da ikon da yankunanta, ya bukaci a tallafawa muhimman ayyukan MDD, kuma a samar da tallafin sake gina kasar domin samun damar warware dambarwar siyasar kasar.

Da yake buga misali game da halin siyasar da ake ciki a kasar, Ma ya ce, kasar Sin tana maraba da irin cigaban da aka samu wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa a Irakin kana ya yaba da kokarin da shugabannin Irakin ke yi wajen warware banbance banbancen dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawar sulhu, da ci gaba da daukar matakan bunkasa tattalin arzikin kasar, da kyautata yanayin zamantakewar rayuwar al'umma kasar, da kuma sake gina hanyoyin ci gaban kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China