in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ce ma'aunin tattalin arzikinta na GDP yana samun bunkasuwa
2019-02-14 10:05:29 cri
A jiya Laraba gwamnatin Najeriya ta ce tattalin arzikin kasar yana samun tagomashi, bisa la'akari da yadda ma'aunin tattalin arzikin kasar na GDP yake matukar ci gaba da bunkasuwa tun bayan da kasar ta fice daga rikicin tattalin arziki a shekarar 2017.

A bisa ga alkaluma na baya bayan nan da hukumar kididdiga ta kasar (NBS) ta fitar a ranar Talata, ma'aunin GDP na kasar ya karu da kashi 2.38 bisa 100 a rubu'in na hudu na shekarar 2018, kuma wannan shi ne karuwa mafi girma da aka samu tun bayan da tattalin arzikin kasar ya shiga mawuyacin hali a shekarar 2016.

A wata sanarwar da aka baiwa kofenta ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Abuja, ministan kula da kasafin kudi da tsare tsare na Najeriyar Udoma Udo Udoma, ya ce, rahoton ya nuna cewa, fannin tattalin arzikin kasar yana samun tagomashi matuka.

A cikin shekara ta 2018 GDPn ya karu daga kasha 0.82 bisa dari a shekarar 2017 zuwa kashi 1.93 bisa dari a shekarar 2018.

Musamman alkaluman karuwar GDPn Najeriyar na baya bayan nan ya nuna cewa, an samu bunkasuwar bangarorin tattalin arzikin kasar ne wadanda bai shafi man fetur ba, kuma ya yi matukar karuwar da ba'a taba samun irinsa ba tun a rubu'in shekarar 2015.

Duk da cewa an samu bunkasuwar tattalin arzikin sauran bangarori a kasar, amma har yanzu, bangaren albarkatun man fetur shi ne hanyar samun kudin shiga mafi girma ga Najeriyar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China